Home Labaru Erling Haaland Na Borussia Dortmand Ya Tafi Jinya

Erling Haaland Na Borussia Dortmand Ya Tafi Jinya

10
0

Dan wasan Borussia Dortmand Erling Haaland zai yi jinyar wasu makonni bayan wani rauni da ya ji a saman cinyar sa, inji kocin kungiyar Marco Rose.

A kwanan nan ne dan wasan ya dawo daga jinya bayan fama da ya yi da matsalar ciwon jijiya, inda har ya zura kwallo biyu a karawar da Dortmund ta doke Mainz da ci 3-1.

Hakan ya ba Dortmund damar darewa kan teburin gasar Bundesliga da ake bugawa a Jamus a karshen makon da ya gabata.

Sai dai a ranar Asabar dinnan Haaland dan shekara 21 ya fuskanci sabon kalubale a karawar da suka yi da Armenia Bielefeld.

Erling Haaland dan asalin kasar Norway, bai samu damar bugawa kasar sa wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba da kasar Turkiyya, da Latvia da Montenegro saboda ba ya iya tafiya sanadiyyar ciwon jijiyar.

Haaland ya ci wa Dortmund kwallaye 70 a wasanni 69 tun bayan da ya koma kungiyar daga Red Bull Salzburg a shekarar 2019.