Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sace Yara Mata Biyu A Jihar Ondo

‘Yan Bindiga Sun Sace Yara Mata Biyu A Jihar Ondo

11
0

Wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun sace wasu ƙananan yara mata daga hannun iyayen su a cikin mota a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Juma’a a yankin Leo.

Maharan sun afka wa iyayen ne a lokacin da mahaifiyar su ke buɗe ƙofar shiga gidan domin ajiye motar su.

Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun je a mota ne kafin su ƙwace motar iyayen yaran su gudu da ita, inda suka bar tasu a wurin.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ta tabbatar wa manema faruwar lamarin a yau Asabar.