Home Labaru Klopp Ya Ce Liverpool Ba Ta Shakkar Haduwar Ta Da Atletico Madrid

Klopp Ya Ce Liverpool Ba Ta Shakkar Haduwar Ta Da Atletico Madrid

9
0

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ko kadan baya shakkar Zubin ‘yan wasan da Diego Simeone zai yi amfani da shi a was an su na yau a gasar cin kofin zakarun Turai.

Jurgen Klopp wanda ya ce Simeone ya yi amfani da dabaru wajen zubin ‘yan was an shi a bara da ya basu damar nasarar kan Liverpool da kwallo 3 da 2 a gasar wanda a wancan lokaci ya fitar da Liverpool bayan jumullar kwallaye 4 da 2 a gida da waje, ya ce ba kadai zubin ‘yan wasan na Simeone ne ya yi tasiri wajen hana Liverpool nasara a wasan ba, harma da matakin hana halartar ‘yan kallo da ya sanya tawagar buga wasan ba tare da cikakken karsashi ba.

Wasan na Liverpool da Atletico Madrid cikin watan Maris din 2020 shi ne wasan farko da aka fara ba tare da ‘yan kallo ba, gabannin dakatar da wasannin dungurugum na tsawon watanni saboda Corona Virus.

Manajan na Liverpool wanda ke amsa tambaya gaban manema labarai gabanin wasan na yau, ya ce tawagar tasa na shirin tunkarar kungiya mafi karfi yanzu a Spain amma dukkaninsu suna da nasu banbance-bambancen.

Liverpool dai zuwa yanzu bata yi rashin nasara a koda wasa guda ba, cikin wasanni 11 da ta doka a wannan kaka.