Home Labaru Miyagun Laifuffuka: ‘Yan Nijeriya 119 Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa A Malaysia

Miyagun Laifuffuka: ‘Yan Nijeriya 119 Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa A Malaysia

220
0

Kungiyar kare hakkin bil-Adama Amnesty International, ta bankado wasu jerin ‘yan Nijeriya 119 da su ke zaman jiran mutuwa a kasar Malaysia.

Wata majiya ta ce, ‘yan Nijeriyar 119, na daga cikin mutane 1,281 da gwamnatin kasar Malaysia ta yanke wa hukuncin kisa sakamakon aikata laifuffuka daban-daban a fadin kasar.

A cikin wani rahoton da ta fitar, Amnesty ta bayyana bukatar a tsawata wa kasar Malaysia ta daina kashe masu laifi, bugu da kari ta nemi kasar ta warware dokar da ta ba ta damar kashe duk wani mutumi da aka kama da aikata miyagun laifuffuka.

Rahoton ya kara da cewa, mutanen da ke jiran a zartar masu da hukuncin kisa da yawan su ya kai 1,281, su na nan an ajiye su a wuraren ajiyar mutane guda 26 da ke fadin kasar.

A karshe kungiyar ta ce, bai kamata a yanke wa mutum hukuncin kisa saboda an kama shi da safarar miyagun kwayoyi ba.