Home Labaru Dimokradiyya: Nijeriya Ta Kama Hanyar Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Tilo –...

Dimokradiyya: Nijeriya Ta Kama Hanyar Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Tilo – APC

220
0

Jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa, Nijeriya ta kama hanyar zama kasa mai jam’iyyar siyasa daya tilo.

APC ta ce, a matsayinta na jam’iyyar da ta yi imani da tsarin dimokradiyya da kuma siyasar kawo sauyi, ba za ta iya ci-gaba da yaudarar kai da cewa komai ya na tafiya lafiya ba.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar Lanre Issa-Onilu ya fitar, APC ta ce tsarin dimokradiyya ba zai tafi yadda ya kamata ba, idan har jam’iyyar adawa ta PDP ta zama maras sanin ciwon kai da rashin alkibla ba.

Ta ce yayin da gwamnati mai ci ke tunkarar hanyoyin magance kalubalen Nijeriya, abin da jam’iyyar PDP da ‘yan kazagin ta su ka fi kwarewa a kai ba wuce karkatar da hankula ba.