Home Labaru Siyasa Fashi Da Makami: An Fille Kan Wani Jami’in Dan Sanda Da Mai...

Fashi Da Makami: An Fille Kan Wani Jami’in Dan Sanda Da Mai Gadi A Jihar Kwara

255
0

Wasu ‘yan fashi da makami sun kai hari wani gidan mai na NNPC da ke yankin Asaba Dam a birnin Illorin na jihar Kwara, inda su ka fille kan wani jami’in dan sanda mai mukamin Sajen da wani mai gadi a gidan man.

Wata majiya ta ce, ‘yan fashin sun kai farmaki ne bayan ma’aikatan gidan man sun tashi daga aiki zuwa gidajen su.

Bincike ya nuna cewa, gidan man ya kasance a rufe tun daga ranar Lahadi, wanda hakan ya sa al’ummar yankin cikin halin fargabar cewa hakan na iya janyo karancin mai a yankin.

Mai Magana da yawun rundunanr ‘yan sanda ta jihar Kwara Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun fara bincike a kan lamarin.