Home Labaru Miyagu Na Amfani Da Sunan Ipob Su Na Kashe Bayin Allah –...

Miyagu Na Amfani Da Sunan Ipob Su Na Kashe Bayin Allah – Gwamnoni

25
0

Kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin Nijeriya, ta ce miyagu su na amfani da sunan kungiyar ‘yan A-Waren IPOB wajen kashe mutanen da ba su ji ba basu gani ba.

Gwamnonin sun bayyana haka ne, yayin da su ka bukaci hukumomin tsaro su kare rayukan al’umman jihar Anambra gabannin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas David Umahi ya fitar.

Ya cej su a matsayin su na gwamnonin kudu masu gabas, sun jajirce domin samar da mafita a kan halin da ake ciki a yankin, kuma za a cimma hakan cikin sauri idan aka dakatar da dokar zaman gida da duk wani rikici a kudu maso gabas.