Home Labaru Ministan Lantarki Ya Kasa Kare Kasafin N42B A Gaban Kwamitin Majalisa

Ministan Lantarki Ya Kasa Kare Kasafin N42B A Gaban Kwamitin Majalisa

107
0

Sabon Ministan Lantarki da Makamashi Abubakar Aliyu ya shiga inda-inda, yayin da ya kasa bada ba’asin yadda za a kashe naira biliyan 42 a kasafin ma’aikatar sa na shekara ta 2022.

Yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Lantarki da Makamashi na Majalisar Dattawa, Ministan ya bijiro da batun za a kashe naira biliyan 42 a aikin tashar wutar Zungeru, sannan ya kira aikin da cewa sabon aiki ne za a yi.

Sai dai Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar Sanata Enyinnaya Abaribe ya taka masa birki, ya na mai korafi a kan yadda Ministan ya kira aikin tashar wutar Zungeru a Matsayin sabuwa, alhalin tuni har an kashe wa aikin naira biliyan 25 a kasafin shekara ta 2021.

Sauran ‘yan kwamitin sun nuna damuwa, tare da cewa ko a kasafin shekara ta 2021 sai da aka tada ƙura a gaban kwamitin game da waɗannan kuɗaɗe.

Ganin yadda ya kasa bada cikakkiyar amsa, nan take Ministan ya bada haƙuri, sannan ya ce kalmar sabon aiki da ya furta kuskuren alkalami ne.