Home Home Mutune 20 Aka Tabbatar Da Sun Mutu A Benen Da Ya Rushe...

Mutune 20 Aka Tabbatar Da Sun Mutu A Benen Da Ya Rushe A Legas

75
0

Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce adadin mutanen da suka mutu a benen da ya ruguje a Ikoyi Lagos ya ƙaru, inda yanzu suka kai mutum 20.

A ranar Litinin ne dogon benen mai hawa 22 ya rushe a unguwar Ikoyi a Legas kudu maso yammacin Najeriya.

Hukumomin Lagas sun ce an ciro ƙarin gawar mutum 14 da suka mutu kuma ana tunanin adadin zai iya ƙaruwa. An kuma yi nasarar ceto mutum tara a raye daga ginin, waɗanda ake kula da su a asibiti.

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya dakatar da shugaban hukumar kula da gidaje ta jihar, yayin da ƴan sanda ke ci gaba da bincike domin gano dalilin rushewar ginin.

An samu rugujewar gine-gine da dama a Lagos a ‘yan shekaru nan.