Home Labaru Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Ya Kamu Da Korona

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Ya Kamu Da Korona

91
0

Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammad Musa Bello, ya kamu da cutar korona.

Mai magana da yawun ministan, Abubakar Sani ne ya tabbatar da haka ga manema labarai.

A wani saƙo da ministan ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewa bayan ya ji alamun rashin lafiya, ya yanke shawarar yin gwaji wanda bayan gwajin aka tabbatar da ya kamu da cutar.

Ministan ya ce a halin yanzu lafiyar sa ƙalau amma yana jin ƙaiƙayi a maƙogwaron sa da kuma jin zazzaɓi da kuma mura mai majina.

Ministan ya kuma bayyana cewa tuni ya killace kan sa inda yake ci gaba da shan magani.

Leave a Reply