Home Labaru Wawure Kudin NDDC: Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Hukunta Wanda Aka Samu...

Wawure Kudin NDDC: Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Hukunta Wanda Aka Samu Da Laifi

89
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ana bibiyar rahoton kudin hukumar raya yankin Niger Delta wato NDDC da zummar dawo da duk wani kobo da ya bata, tare da gurfanar da duk wanda aka kama da sama da fadi kan kudin.

Da yake magana wajen wani taro na hukumar a jami’ar Uyo dake Akwa Ibom, Shugaba Buhari ya ce abin takaici ne yadda wasu mutane tsiraru suka cinye kudaden da aka aike wa yankin cikin kusan shekara 20 domin bunkasar sa, suka jefa mafi yawa cikin yanayi mara dadi.

Shugaban kasa ya ce hukumar na bukatar cimma manufofin da aka kirkireta akai, domin samar da sauyi mai inganci ga rayuwar mutanen yankin Niger Delta.

Ya ce Rayuwar mutanen yankin za ta iya inganta sama da yadda take yanzu, da ace ana tafiyar da wadannan kudaden da ake aikewa sama da shekara 20.

RAHOTO- KATSINA 1

Leave a Reply