Home Labaru Yawan Mutanen Da Suka Kamu A Najeriya Ya Kai 241,513

Yawan Mutanen Da Suka Kamu A Najeriya Ya Kai 241,513

61
0

Hukumar daƙile yaduwar cutuka a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 1,139 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasa ranar Alhamis 30 ga watan Disamba 2021.

Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Ribas ce ta fi yawan mutane inda take da 420 sai Legas mai 324, sai Oyo inda aka sami 81 sai Gombe mai 47 yayin da Akwa Ibom ke da 41.

Sauran su ne jihar Kaduna mai mutum 36, sai jihar Neja inda aka samu mutum 36 sai Ondo mai 35, sai Abuja babban birnin tarayya mai 29, sai kuma Delta mai 18.

Jihar Edo na da mutum 15 kuma Ogun na bi ma ta da 14, inda Kano ke da mutum 12, jihar Cross River na da 9, Ekiti da Kebbi na da takwas-takwas, Nasarawa kuwa na da 4, su kuma jihohin Enugu da Jigawa na da mutum daya-daya kawai.

Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai 241,513 amma kuma an sallami 214,003 daga asibiti.

Yawan waɗanda suka rasa rayukan su sanadin cutar ta korona kuwa ya kai 3,030.