Home Labaru Maulidi: Shugaba Buhari Ya Taya Daukacin Al’ummar Nijeriya Murna

Maulidi: Shugaba Buhari Ya Taya Daukacin Al’ummar Nijeriya Murna

732
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce babban abin da musulmi za su yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W.) ita ce dabbaka koyarwar sa a rayuwar su da zamantakewar su.

Buhari ya wallafa sakon ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce satar jama’a domin neman kudin fansa da kisan jama’a da yi wa mata auren dole duk sun saba da koyarwar addinin musulunci.

Ya ce ya na taya daukacin musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (S.A.W.), ya na mai cewa babbar girmamawar da musulmi za su yi wa Annabi ita ce dabbaka halayen sa na rashin son tada zaune tsaye da son zaman lafiya da kuma yin hakuri.

Buhari ya kuma kara da jan hankalin musulmi, su maida hankali wajen yakar akidojin da ke sa tsananin kishin addini da ka iya jefa mutane cikin yanayin ta’addanci.