Home Labaru Ranar Murna: Ina Taya Dan’uwa Na Mamman Daura Murnar Cika Shekaru 80...

Ranar Murna: Ina Taya Dan’uwa Na Mamman Daura Murnar Cika Shekaru 80 – Buhari

302
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon taya murna ga Dan-Uwan sa Mamman Daura da ya cika shekaru 80 a duniya.

Buhari ya yi addu’a, tare  da yi wa Mamman Daura fatan alkhairi a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Mamman Daura, wanda ya ke da ne ga shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekaru 80 ne a ranar 9 gawatan Nuwamba.

Mamman Daura, fitaccen dan Jarida ne da ya yi aiki a jaridar New Nigeria a Kaduna, inda ya kai ga matsayin babban darakta kafin ya bar aiki ya koma harkokin kan sa, sannan ya kafa kamfanoni da dama da kuma hannu wajen kafa masaku a Kaduna.

Sunan Mamman Daura dai ya fito karara ne tun bayan darewa kujerar shugabancin Nijeriya da kawun sa shugaba Muhammadu Buhari ya yi.