Home Labaru Siyasar Amurka: Mai Kudin Duniya Zai Yi Takara Da Donald Trump

Siyasar Amurka: Mai Kudin Duniya Zai Yi Takara Da Donald Trump

705
0

Mai kudin duniya na 14 Michael Bloomberg, ya na sake shinshinar kujerar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Democrats.

Attajirin, wanda tsohon magajin garin birnin New York ne, ya ce ya na da shakku wajen mutanen da ke son fitowa takara domin ba za su iya kada Donald Trump a zaben shekara ta 2020 ba.

Ana dai sa ran dan kasuwar mai shekaru 77, zai gabatar da tsare-tsaren sa domin neman cin zaben cikin gida da za a yi a Alabama.

Sai dai shugaba Trump ya yi wa Michael Bloomberg ba’a, inda ya ce idan akwai mutumin da ya ke son takara da shi shi ne Michael wanda karamin alhaki ne.

Mutane 17 ne dai ke takarar kujerar shugabancin a jam’iyyar Democrat, kuma tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, da Senator Elizabeth Warren da Senator Bernie Sanders su ne a gaba-gaba.