Home Labaru Matsayar Gwamnati: Abin Da Ya Sa Muka Saki Sambo Dasuki Da Sowore...

Matsayar Gwamnati: Abin Da Ya Sa Muka Saki Sambo Dasuki Da Sowore – Malami

891
0
Ministan shari’a Abubakar
Ministan shari’a Abubakar

Ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce jin kai da biyayya ga umarnin kotuna ne dalilan da su ka sa gwamnati ta saki Sambo Dasuki da mawallafin jaridar Sahara Reporters Omowole Sowore.

Abubakar Malami, ya ce gwamnati ta ga dacewar yin biyayya ga umarnin kotunan Nijeriya da su ka bada belin Sambo da Sowore, duk da cewa su na da damar ci-gaba da tsare su saboda sun kalubalanci matakin kotunan.

Ya  ce ba wani dalilin da za a iya bayyanawa a matsayin hujja bayan na sha’awa da da’a da abin da ya danganci doka da umarnin kotu.

Ministan ya kara da cewa, an saki mutanen biyu ne bisa dalilai na jin kai, duk da yake gwamnatin tarayya tana da hakki na ta ci gaba da rike su a lokacin da take kalubalantar sakinsu, har a kai matika ga kotun koli.”