Ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce jin kai da biyayya ga umarnin kotuna ne dalilan da su ka sa gwamnati ta saki Sambo Dasuki da mawallafin jaridar Sahara Reporters Omowole Sowore.
Abubakar Malami, ya ce gwamnati ta ga dacewar yin biyayya ga umarnin kotunan Nijeriya da su ka bada belin Sambo da Sowore, duk da cewa su na da damar ci-gaba da tsare su saboda sun kalubalanci matakin kotunan.
Ya ce ba wani dalilin da za a iya bayyanawa a matsayin hujja bayan na sha’awa da da’a da abin da ya danganci doka da umarnin kotu.
Ministan
ya kara da cewa, an saki mutanen biyu ne bisa dalilai na jin kai, duk da yake
gwamnatin tarayya tana da hakki na ta ci gaba da rike su a lokacin da take
kalubalantar sakinsu, har a kai matika ga kotun koli.”