Home Labaru Difilomasiyya: Osinbajo Ya Bar Nijeriya Don Halartan Taro Ecowas A Kasar Guinea

Difilomasiyya: Osinbajo Ya Bar Nijeriya Don Halartan Taro Ecowas A Kasar Guinea

17
0
Osinbajo-travelling

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai wakilci shugaba Muhammadu Buhari a babban taro na musamman na shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar ECOWAS kan yanayin siyasa a Jamhuriyar Guinea.

Babban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa ta fuskar yada labarai Laolu Akande ya bayyana haka.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata, Osinbajo ya halarci babban taron ECOWAS a kan yanayin siyasa a Guinea da Mali, wanda aka gudanar ta yanar gizo a ranar 8 ga watan Satumba.

Taron na zahiri da zai gudana dai zai sake nazarin halin da ake ciki a Guinea, dangane da rahoton babban taron kungiyar ECOWAS zuwa Conakry.

Osinbajo, ya bar Abuja bisa rakiyar karamin ministan harkokin waje Ambasada Zubairu Dada, kuma ana sa ran zai dawo Abuja daga baya a ranar Alhamis din nan.