Home Home Matsaya: Jam’iyyar APC Ta Tura Kujerar Shugabancin Jam’iyya Ga Yankin Arewa

Matsaya: Jam’iyyar APC Ta Tura Kujerar Shugabancin Jam’iyya Ga Yankin Arewa

55
0
Jam’iyyar APC ta tura kujerar shugabancin jam’iyyar ga yankin Arewacin Nijeriya.

Jam’iyyar APC ta tura kujerar shugabancin jam’iyyar ga yankin Arewacin Nijeriya.

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna da Atiku Bagudu na jihar Kebbi su ka bayyana haka, yayin da su ke amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari game lamurran jam’iyyar.

El-Rufa’i, ya ce jam’iyyar APC ta amince da sauya mukaman da babu kowa kan su a kwamitin ayyuka na kasa tsakanin sassan Arewa da Kudanci gabanin taron gangamin ta na kasa a ranar 26 ga watan Maris.

Gwamnonin sun ce, sun amince da tsarin shiyya-shiyya ga duk shiyyoyin siyasar Nijeriya shida, inda shiyyoyin Arewa za su dauki mukaman da shiyyoyin Kudu ke rike da su shekaru takwas da su ka gabata.

Takaitaccen taron dai ya gudana ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, wanda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni 19.