Home Home Tsautsayi: Jami’an Civil Defence 4 Sun Mutu Bayan Sun Taka Nakiya A...

Tsautsayi: Jami’an Civil Defence 4 Sun Mutu Bayan Sun Taka Nakiya A Jihar Neja

67
0
Hukumomi sun ce, wata fashewa ta yi sanadiyyar ajalin wasu jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence huɗu bayan sun taka nakiya a lokaci su ke sintiri a yankin Galadiman Kogo a jihar Neja.

Hukumomi sun ce, wata fashewa ta yi sanadiyyar ajalin wasu jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence huɗu bayan sun taka nakiya a lokaci su ke sintiri a yankin Galadiman Kogo a jihar Neja.

Mai magana da yawun rundunar Odumosu Olusola, ya ce direban motar ne kawai ya tsira, amma ya na cikin mawuyacin hali.

Mazauna yankin sun ce, an dasa nakiyar ne da nufin hana jami’an tsaro shiga yankin da ke fuskantar hare-hare.

Jihar Neja dai ta na cikin yankunan da ke fama hare-haren ‘yan bindiga masu satar mutane.