Home Labaru Matsaya: Gwamnati Ba Za Ta Sake Bari A Taba Kudin Kananan Hukumomi...

Matsaya: Gwamnati Ba Za Ta Sake Bari A Taba Kudin Kananan Hukumomi Ba – Boss Mustapha

904
0
Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta sake bari a taba kudaden kananan hukumomi ba.

Boss Mustapha ya jadadda kudirin gwamnatin tarayya na raba asusun hadin gwiwa na gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi.

Sakataren ya bayyana haka ne, yayin wani taron kula da kananan hukumomi da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Babban daraktan kula da ayyukan musamman da ya wakilci sakataren a wajen taron David Attah, ya zargi gwamnatocin jihohi da tatse asusun da aka tanada domin kananan hukumomi.

Ya ce akwai bukatar kananan hukumomi su samu cin gashin kai da kuma ‘yancin gudanar da al’amuran kudi da aka tanadar masu, lamarin da ya ce hakan zai ba su damar biyan bukatun al’ummomin su tun daga tushe.