Home Labaru Kin-Jinin-Baki: An Sanar Da Ranar Da Za A Fara Kwaso ‘Yan Nijeriya...

Kin-Jinin-Baki: An Sanar Da Ranar Da Za A Fara Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Afrika Ta Kudu

226
0

Gwamnatin tarayya, ta ce Nijeriya za ta fara kwaso ‘yan kasar ta daga kasar Afrika ta Kudu a ranar 7 ga watan Satumba na shekara ta 2019.

Ma’aikatar harkokin waje ta fitar da sanarwa, ta na mai yaba wa wanda ya bada gudunmuwar jirgin sa domin kwaso mutaneb Cif Allen Onyema.

A cewar sanarwar, ‘yan Nijeriya da ke da ra’ayin dawowa gida su gabatar da cikakkun sunayen su, da kauyukan su da kananan hukumomin su da jihohin su da kuma magadan su.

Haka kuma, za su bada lambobin wayoyin su kwafi na fasfon su ko kuma katin shaidar su da kuma hoton fasfo guda biyu, sai dai

Ma’aikatar ta ce duk dan Nijeriyan da ba ya da katin shaidar ma zai iya shiga cikin jerin masu dawowa gida.