Home Labaru Cin Zarafi: An Yanke Ma Wasu Jami’an Sojin Sama Biyu Hukuncin Dauri...

Cin Zarafi: An Yanke Ma Wasu Jami’an Sojin Sama Biyu Hukuncin Dauri A Gidan Yari

599
0
Ibikunle Daramola, Kakakin Rundunar sojin Sama Ta Nijeriya
Ibikunle Daramola, Kakakin Rundunar sojin Sama Ta Nijeriya

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta ce ta tura wasu jami’an ta biyu gidan yari, bayan an gan su a cikin wani faifan bidiyo su na dukan wani farar hula.

A cikin wani faifain bidiyo da ya kewaya a dandalin sada zumunta da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo, an ga sojojin biyu su na dukan wani farar hula da bulala.

Kakakin rundunar sojin sama ta Nijeriya Ibikunle Daramola, ya ce an gurfanar da jami’an, an kuma tabbatar da sun aikata laifin da ake tuhumar su da shi.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar na Twitre, Daramola ya ce an gurfanar da jami’an biyu a gaban wata kotun sojoji da ke sansanin rundunar a Abuja, bayan an gan su a cikin wani faifan bidiyo su na dukan wani farar hula a ranar 30 ga watan Agusta.

Laifin jami’an dai ya saba wa sashe na 104 na kundin dokokin rundunar soji na shekara ta 2004, do haka an yanke masu hukuncin dauri a gidan yarin sojoji tare da horo mai tsanani, bisa umarnin shugaban rundunar na kasa Air Marshal Abubakar Sadiq.