Home Labaru Matsalolin Tsaro: Zuwa 2023 APC Za Ta Gama Ruguza Najeriya —Hakeem...

Matsalolin Tsaro: Zuwa 2023 APC Za Ta Gama Ruguza Najeriya —Hakeem Baba Ahmed

46
0

Kungiyar Dattawan Arewa, ta yi zargin cewa nan da zuwa shekarar 2023, jam’iyyar APC mai mulki za ta karasa ruguza kasar nan.

Kakakin Kungiyar, Dokta Hakeem Baba Ahmed ne bayyana hakan yayin hirarsa a shirin Siyasa wanda Gidan Talabijin na Channels ya yada

Baba Ahmed, ya ce jam’iyyar da za ta karbi mulki daga hannun APC za ta gamu da babban kalubale.

Ya bayyana cewa matsalar tsaro da ake fama da ita a halin yanzu yana da nasaba ne da gazawa a bangaren shugabanci.

Ya nanata cewar matsalolin da ake fuskanta a kasar sun zarta ta’addanci da satar mutane muni.

Ya kara da cewar me za a yi da 2023 saboda daga yanzu zuwa 2023, APC ta gama lalata kasar nan gaba daya?”

Bayanai sun tabbatar da cewa a yanzu haka Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihin kasar.