Home Labaru Zargin Batanci: An Soma Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara A Birnin Kano

Zargin Batanci: An Soma Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara A Birnin Kano

34
0

Wata kotun shari’ar musulunci da ke birnin Kano ta dage shari’ar malamin Addinin Musulunci na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Jami’an gidan gyaran hali ne suka kai malamin kotu da safiyar yau domin a fara shari’arsa a kotun wadda mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ke jagoranta.

Ranar Juma’a 16 ga watan yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano a  bangaren Sheikh Abduljabbar, lauyoyinsa sun hada da Sale Mohammad Bakaro, da sauransu.

Zuwa yanzun dai rahotanni sun tabbatar  da cewar an dage shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Agusta na wannan shekarar domin ci gaba da shari’ar.