Home Labaru Kalubalen Tsaro: ISWAP Ta Kashe Wani Soja Da Ma’aikatan Gwamnati

Kalubalen Tsaro: ISWAP Ta Kashe Wani Soja Da Ma’aikatan Gwamnati

34
0

Kungiyar ISWAP ta yi awon gaba da wani soja da ma’aikacin Gidan Gwamnatin Jihar Yobe da wasu mutum biyu.

A ranar Asabar ne mayakan ISWAP suka yi garkuwa da wasu mutum uku, ciki har da sojan mai suna Las Kofur Oyediran Adedotun a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Shi kuma ma’aikacin gidan gwamnatin ba a san inda yake ba sai daga baya ISWAP ta fitar da hotonsa da katin shaidarsa da na sauran wadanda ta sace.

Sauran mutanen da maharan suka nuna katin shaidarsu har da wani Mustapha Lawan, ma’aikacin Hukumar Kula da Filin Jiragen Sama na Tarayya (FAAN).

Bayan an yada hotunan ne wani ma’aikacin Gidan Gwamnatin Jihar Yobe a Damaturu, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar wa majiyarmu cewa ya ga hoton daya daga cikin ma’aikatansu, Ali Shehu a ciki.

Ya kara da cewa ma’aikacin kuma Jami’in Tuntuba na Yobe Lodge a Maiduguri, Ali Shehu wanda aka fi sani da Mai Lalle; ya bar Damaturu zuwa Maiduguri da tsakar ranar Asabar.