Home Labaru Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Ya Bukaci Al’umma Su Kara Hakuri

Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Ya Bukaci Al’umma Su Kara Hakuri

346
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya roƙi Al’ummar ƙasar nan su ƙara haƙuri game da matsalolin tsaro da ake fuskanta, inda ya ce yana bakin ƙoƙarinsa wurin sayo ƙarin makamai don ƙarfafa ayyukan tsaro.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, yana mai cewa tuni suka sayo wasu makaman.

Buhari yace gwamnati na matuƙar ƙoƙari wurin inganta harkokin tsaro a wasu sassan kasar nan kuma ana kashe kuɗi masu yawa wurin sayen makamai.

Har ila yau ya roƙi jama’a da su ƙara haƙuri kan maganar sayen makamai musamman saboda tasirin annobar korona kan ƙasashen da ke samar da su.

A baya-bayanan dai jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto suna fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu amfani da babura inda suka kashe ɗaruruwan mutane.