Home Labaru Hare-Haren Yemen: Rayukan Mata Da Kananan Yara Sun Salwanta

Hare-Haren Yemen: Rayukan Mata Da Kananan Yara Sun Salwanta

194
0
Rikicin Jukun Da Tiv
Rikicin Jukun Da Tiv

Akalla mutane 20 ne ciki har da mata da kananan yara suka rasu a laradin Jawf da ke karkashin jagorancin mayakan ‘yan tawayen Houthi a arewacin Yemen.

Rahotanni sun ce sojojin hadin gwiwar da ke yaki da ‘yan tawayen karkashin jagorancin Saudiyya ne suka kaddamar da harin, kana kuma ko baya ga mutuwar an bayyana cewa wasu mutum bakwai suka ji rauni.

Kungiyar agaji ta Save the Children mai kula da yara a kasar ta ce akalla yara bakwai ne suka gamu da ajalin su sakamakon hare haren da ake kaiwa kan jama’a a kasa da wata daya a kasar ta Yemen wacce yaki tsakanin gwammnatin kasar mai samun goyon bayan Saudiyya da ‘yan tawayen Huthi ya daidaita.