Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya jagoranci taron gaggawa na kwamitin tsaro na ƙasar inda suka tattauna kan matsalolin tsaro a ƙasar musaman a Jihar Tillabery.
Daga cikin matakan da zaman ya ɗauka akwai batun sa dokar ta-ɓaci a faɗin jihar ta Tillabery.
Hakan ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai ranar Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas – ‘yan Nijar biyu da Faransawa shida.














































