Home Labaru Garkuwa Da Mutane: An Sace Wani Malamin Jami’a A Kaduna

Garkuwa Da Mutane: An Sace Wani Malamin Jami’a A Kaduna

287
0

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da cewa wasu masu garkuwa da mutane sun dauke wani malamin Jami’ar gwamnatin Tarayya dake Dutsinma, a jihar Katsina.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo,

Wanda aka yi garkuwa da shin, wato Abubakar Idris, mazaunin Garin Barnawa ne dake karamar hukumar kaduna ta kudu a jihar Kaduna.

Yakubu Sabo, ya ce babban jami’i a ofishin ‘yan sanda na  Barnawa DPO ya sanar da su cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun tafi da Abubakar Idris a gidan sa dake titin Lawal Ahmad a Barnawa Kaduna.

DPOn ya ce ko kafin su isa wurin masu garkuwan sun gudu da shi, sai dan an gano cewa masu garkuwan sun biyo shi ne tun daga wani wuri har zuwa gidan sa wajen karfe ɗayan dare.

Yakubu Sabo ya ce tuni har su tura jami’an su domin ganin an bankado waɗannan masu garkuwa da mutanen.