Home Labaru Afrika Ta Kudu: An Yi Wa Jacob Zuma Afuwa Saboda Rashin Lafiya

Afrika Ta Kudu: An Yi Wa Jacob Zuma Afuwa Saboda Rashin Lafiya

57
0

An saki tsohon shugaba Afrika Ta Kudu Jacob Zuma daga gidan yari bisa dalilin rashin lafiya.
Sai dai zai ci gaba da zaman kason nasa ne a gidansa ƙarƙashin sa idon hukumomi.
Hukumar kula da gidajen yari ta ƙasar ta ce an yi wa Mista Zuma tiyata a watan jiya kuma yana samun kulawa a asibiti a halin yanzu.

Wannan na zuwa kusan wata biyu bayan da tsohon shugaban ya fara zaman gidan yari na wata 15, bisa laifin raina kotu bayan da ya ƙi bayyana a gabanta domin sauraren ƙarar cin hanci da rashawa da ake yi kansa.

Tsare shi da aka yi ya janyo mummunar zanga-zanga da ta rikiɗe zuwa kashe-kashe da ɓalle shaguna a lardinsa na Kwa-Zulu da kuma a Gauteng.
A watan Yuli ne Mr Zuma ya miƙa kansa ga hukumomi, bayan da alƙali ya ba da umarnin kama shi saboda ƙin halartar zaman da ake yi na tuhumar cin hanci lokacin mulkinsa.

Duk da ya rasa kujerarsa da kuma ƙarfin faɗa aji a jam’iyyarsa ta ANC a 2018, har yanzu Jacob Zuma na da ɗimbin magoya baya a Afrika Ta Kudu, musamman ma a yankin KwaZulu-Natal inda ya fito.