Home Labaru Matashiyar Da Ta Cinna Wa Kan Ta Wuta A Zamfara Ta Rasu

Matashiyar Da Ta Cinna Wa Kan Ta Wuta A Zamfara Ta Rasu

1005
0

Matsashiyar nan mai suna A’isha Aminu da ke unguwar  Albarkawa a jihar Zamfara, wadda ta cinna wa kan ta wuta saboda an hana ta auren saurayin da ta ke kauna ta riga mu gidan gaskiya.

A’isha, ta rasu ne a ranar Larabar nan, bayan fama da jinya ta sama da wata guda sakamakon raunukan da ta samu bayan cinna wa kan ta wuta.

Wani makwafcin marigayiyar ya shaida wa manema labarai cewa tuni an yi jana’izar ta.

Kafin rasuwar ta, A’isha ta shaida wa manema labarai cewa, ta dauki matakin kona kan ta ne saboda ba za ta iya hakura da saurayin ba.

Mahaifin Amarigayiyar Aminu Muhammad Albarkarawa, ya ce saurayi ne take so tsawon shekara daya amma Allah bai sa ya na da abin auren ta ba.