Home Labaru An Yi Garkuwa Da Alkalin Babbar Kotun Tarayya Abdul Dogo

An Yi Garkuwa Da Alkalin Babbar Kotun Tarayya Abdul Dogo

249
0

Masu garkuwa da mutane, sun yi awon gaba da Alkalin babbar kotun tarayya da ke birnin Akure na jihar Ondo mai shari’a Abdul Dogo.

An dai sace Alkalin ne, yayin da ya ke hanyar komawa Akure daga Abuja.

Wata majiya ta ce an samu rahoton cewa, masu garkuwar sun tuntubi iyalan Alkalin, sun kuma bukaci Naira milliyan 50 a matsayin kudin fansa.

Tuni da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya ya tura tawagar  DCP Abba Kyari zuwa Akure domin ceto Alkalin.