Home Labaru Magance Rikici: Za A Gina Rugagen Fulani 57 A Jihar Jigawa

Magance Rikici: Za A Gina Rugagen Fulani 57 A Jihar Jigawa

358
0

Gwamnatin jihar Jigawa, ta ce za ta gina rugagen Fulani 57 a sassan jihar, domin rage yawan tashin hankali da rikici da ke barkewa tsakanin makiyaya da manoma.

Mataimakin gwamnan jihar Umaru Namadi ya sanar da haka a wani zama da aka yi da jami’an tsaro a jihar, inda ya ce gwamnati za ta gina rijiyoyin burtsatse a duk wadannan rugaggen, sannan ta raba wa shugabannin makiyaya da manoma baburan hawa guda 62.

Namadi, ya yi kira ga manoma da makiyaya Fulani su guji yi wa doka karan tsaye a jihar, ya na mai cewa su rika zama da juna lafiya.

Kwamishian ‘yan sanda na jihar Bala Sanchi, ya ce ci-gaban kowace kasa ya dogara ne da zaman lafiya, amma hakan ba shi ke faruwa a jihar ba, saboda matsalar rashin jituwa tsakanin Fulani da manoma.