Home Labaru Matasan Arewa A Kudu Sun Nemi Shugabannin Arewa Su Hada Kai

Matasan Arewa A Kudu Sun Nemi Shugabannin Arewa Su Hada Kai

72
0

La’akari da yadda ake ganin yankin Arewa ya samu koma-baya ta kowanne fuska idan aka kwatanta da yankin kudu, wasu matasa sun fara kiraye-kiyare ga shugabannin yankin su samar da mafita tare da haɗa kansu tun kafin dare ya yi musu.

Shugaban matasan Arewa da ke zaune a Legas, Ibrahim Ya’u Sule, ya yi kira ga masu riƙe da madafun iko a yankin Arewa su kawo mafita ga matsalolin Arewa tare da gina yankin tun kafin lokaci ya ƙure musu.

Shugaban matasan ya ƙara da cewa yankin Kudancin Nijeriya suna da ƙungiyoyin da suke kare maradun su fiya da Arewa, ya ce mutanen Kudu suna amfani da damar da suke da shi wajen taimaka wa al’ummar su, amma shugabannin Arewa ba sa yin haka.

A cewar sa, ya kamata shugabannin Arewa su tashi daga dogon barci wajen ɗaukan matakai da suka dace, su daina tunani kan mulki wanda suka tare a Abuja su da ‘ya’yan su, su sani wata rana za su bar karagar mulki kuma wannan masifar zai iya shafar su.