Home Labaru INEC Ta Nemi Amincewar Shugaban Kasa

INEC Ta Nemi Amincewar Shugaban Kasa

63
0

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar da batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.

INEC ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ne ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro, dangane da kudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙe jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwani na ‘yan takara.

A ranar 29 Ga Nuwamba ce Majalisar Dattawa ta aika wa Shugaba Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka, ya na da kwana 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu, domin ya tabbata doka, wanda sabon ƙudirin matukar Shugaba Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓen ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.

A cikin kwaskwarimar dai an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara, Sai kuma batun aiko sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga shuagab Buhari, kan batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓen su ka ƙunsa.