Home Labaru Gwamna Zulum A Najeriya Ya Hana Ba Da Agaji A Borno

Gwamna Zulum A Najeriya Ya Hana Ba Da Agaji A Borno

115
0

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya haramta bayar da tallafin kayayyaki ciki har da na abinci ga dubban wadanda gwamnati ta mai da su yankunansu na sali.

A cewar gwamnan na jihar Borno, Babagana Umara Zulum, maimakon ba su kayayyakin da sunan agaji, kamata ya yi a ba su horon sanin yadda za su sama wa kan su abinci, ba kuma mika musu abincin ba.

To sai dai fa matakin na gwamnatin jihar Borno, ya ci karo da suka daga kungiyoyin agaji da dama da ke a jihar, suna mai cewa jihar na dauke da dubban mabukata tallafi.

Gwamnatin jihar Bornon dai ta mai da mutane da dama da rikicin Boko Haram ya raba da muhallan su Gida.