
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) tace akalla matasa 172 suka samu tabin hankali saboda Shan miyagun kwayoyi a Jihar Zamfara.
Mataimakin Shugaban Hukumar Ladan Hashim ne ya sanar da hakan inda yace an samu wannan adadin ne a cikin shekara shida da suka gabata.
Ladan ya ce, yanzu haka akwai “Matasa da dama dake tsare a gidajen yari, da gidajen kula da lafiya, inda suke fama da cututtukan kansar makogwaro da cutar hanta da cutar koda da sauransu, sakamakon shaye-shaye.
Ya ce a cikin wata taran da suka gabata hukumar ta tsare mutum 221 kan shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.
Har ila yau yace akwai bukatar samun hadin kai, fahimta da taimako domin magance matsalar.
Daga karshe ya bukaci Al’umma su rika amfani da magunguna yadda ya dace bisa umurnin kwararrun likitoci dam asana fannin kula da lafiya.













































