Home Labaru An Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato

An Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato

12
0

Rahotanni daga Jos, babban birnin jihar Filato sunce ‘yan majalisar dokokin jihar sun tsige shugabansu Abok Ayuba daga mukaminsa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya rawaito cewa ‘yan majalisa takwas ne cikin 24 ne suka cire shugaban majalisar dokokin a ranar Alhamis din nan.

A zaman da suka yi wanda mataimakin shugaban majalisar Saleh Yipmong ya jagoranta, sun zabi Yakubu Sanda a matsayin sabon shugaban majalisar.

Bayanai sun ce ‘yan majalisar sun yi yunkurin cire shugabansu ne a ranar Laraba da daddare amma hakan bata yiwu ba, lamarin da ya sa suka yi sammako da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Wasu rahotanni sun ce ‘yan majalisar sun dauki matakin ne sa’ilinda jami’an tsaro suka kewaye Ginin Majalisar.