
Kwamitin majalisar Dattijai kan harkokin cikin gida ya fara yunkurin ganin an kara wa fursunonin da ke gidajen gyaran hali kudin abinci.
Lamarin fara ne a ranar Laraba sa’ilinda da shugaban gidajen yarin kasar nan Haliru Nababa ya bayyana gaban kwamitin domin kare kasafin kudin hukumar kula da gidajen yari na shekarar 2022.
A cewar kwamitin, akwai fursunoni 66,340 a gidajen gyaran hali da ke fadin kasar nan, kuma daga cikinsu akwai mutum 47,559 dake jiran shari’a.
A yayin zaman ne Sanata Utazi, ya gabatar da shawarar cewa ya kamata a rika baiwa kowane fursuna Naira 750 domin sayen abinci.
A nasa martanin, shugaban hukumar kula da gidajen yarin ya ce an kara kudin kashewar fursunonin daga Naira 450 zuwa Naira 750 a kowacce rana a cikin kasafin kudin 2022.













































