An samu hargitsi a majalisar wakilai, tsakanin matan sabon
kakakin majalisar Abbas Tajudeen.
Lamarin dai ya faru ne lokacin da sabon kakakin majalisar ya
ke karbar rantsuwar kama aiki, inda matan su ka nemi su ba
hammata iska a dandamalin majalisar.
Rahotanni sun ce, komai ya na tafiya daidai lokacin da aka
kira Abbas zuwa kan dandamalin majalisar domin ya yi
rantsuwar kama aiki a matsayin sabon kakakin majalisar
wakilai.
Tajuddeen Abbas dai ya na tare da ɗaya daga cikin matan sa
ne a ɓangaren dama, sai dai ana cikin rantsuwar kawai sai
ɗaya matar ta hau ta janyo hargitsi, inda ta ture kishiyar ta
daga gefen mijin su.
Lamarin dai ya yi matuƙar ba Tajuddeen Abbas mamaki, inda
ya dakatar da rantsuwar ya bulbuleta da faɗa a kan abin
kunyar da ta aikata.














































