Home Labaru Mun Kunyata Masu Cewa Ba Za Mu Yi Nasara Ba – Tajuddeen...

Mun Kunyata Masu Cewa Ba Za Mu Yi Nasara Ba – Tajuddeen Abbas

306
0

Sabon shugaban Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas, ya ce
nasarar da ya samu ta zama Kakakin Majalisar wakilai ta
kunyata masu surutai da gulmar cewa ba zai iya yin nasara ba.

Da ya ke magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Tajuddeen ya ce akwai mutanen da ke cewa ba ya da magoya baya, saboda wai jam’iyya ce ta ƙaƙaba shi.

Tajuddeen Abbas dai ya je Fadar Shugaban Ƙasa ne bisa rakiyar Mataimakin sa Bejaminn Kalu, inda su ka je domin kai ziyarar godiya ga Shugaba Bola Tinubu bayan sun samu nasarar zaɓen.

Idan dai baa manta ba, tun a cikin watan Mayu ne Tinubu ya nuna Tajuddeen Abbas da Bejamin Kalu ya ke goyon baya, kamar yadda jam’iyyar APC ta ce ta na goyon bayan ‘yan majalisar biyu.

Tajuddeen Abbas, ya ce sun kunyata masu ganin cewa jam’iyyar APC ce ta ƙaƙaba su a kan muƙamin, musamman masu cewa ba su da masu goyon baya.

Leave a Reply