Bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban
hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, Abdulkarim
Chukkol ya zama shugaban riƙo na hukumar.
Kafin wannan lokacin dai, Abdulkarim Chukkol ya na riƙe da muƙamin daraktan gudanarwa a hukumar.
Abdulkarim Chukkol ƙwararre ne a harkar bincike, kuma ya gwanance a ɓangaren binciken ayyukan zamba ta yanar gizo da halasta kuɗaɗen haram.
Chukkol ya kammala karatun digirin sa ne a Jami’ar Maiduguri a shekara ta 2000, sannan ya yi karatun difloma a fannin shari’a a Jami’ar Virginia da ke kasar Amurka a shekara ta 2011.














































