Home Labaru Kiwon Lafiya Annobar Korona: Mutum Uku Sun Mutu, 501 Sun Kamu Ranar Lahadi A...

Annobar Korona: Mutum Uku Sun Mutu, 501 Sun Kamu Ranar Lahadi A Najeriya

114
0

Hukumar daƙile yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 501da suka kamu da cutar korona a ranar Lahadi a Najeriya sannan ƙarin wasu mutum uku sun mutu.

Hukumar t ace cikin wadanda suka karun Jihar Legas ce ke da adadi mafi yawa da mutun 218, yayin da Abuja ke bi mata da mutum 112.

Kaduna na da mutum 53, sai Plateau mai mutum 24, sai Katsina mai 21, Jihar Kano na da mutum 16, sai kuma Yobe mai mutum 14, Ondo an samu mutum 10 sai Ogun mutum 9, Edo mutum 7, sai Bayelsa mai mutum 5.

Jihohin Rivers da Borno na da mutum4-4, yayin da Osun da Ekiti suka rufe jadawalin da mutum 2-2 kowannen su.

A jimillance adadin mutunen da cutar ta kama tun daga bullarta zuwa yanzu sun kai dubu 78 da 434, yayin da dubu 68 da 303 suka warke aka kuma samu asarar rayukan mutum dubu 1 da 221.