Home Labaru Matakan Tsaro: An Toshe Layukan Sadarwa A Wasu Sassan Jihar Katsina

Matakan Tsaro: An Toshe Layukan Sadarwa A Wasu Sassan Jihar Katsina

13
0
SADARWAA

Gwamnati ta bada umurnin toshe layukan sadarwa a wasu sassa na jihar Katsina, kusan mako guda kenan bayan an toshe na jihar Zamfara da ke makwaftaka da ita.

Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara a kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmed Katsina ne ya tabbatar da batun katse layukan inda ya ce an ɗauki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.

Yace Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Funtua da Bakori da Jibiya da Malumfashi da Faskari da Batsari da Ɗanmusa.

Sauran kuwa su ne Sabuwa da Kankara da Dutsinma da Kurfi da Safana da Ɗandume.

A cewar Ibrahim Ahmad Kastina, ya zama wajibi gwamnatin Katsina ta ɗauki wannan mataki, domin hana ƴan bindigar da ke Zamfara gangarawa Katsina su ci gaba da amfani da waya dan gudanar da harkokin su.