Home Labaru Yajin Aiki: ASUU Na Barazanar Sake Komawa Gidan Jiya

Yajin Aiki: ASUU Na Barazanar Sake Komawa Gidan Jiya

14
0
ASUU

Kungiyar Malaman Jami’oi ta Najeriya ASUU ta zargi Gwamnatin Tarayya da kin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a watan Disambar bara.

Jami’in kungiyar na shiyyar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad ya sanar da hakan yayin da yake jawabi ga wani taron manema labarai yau a Kano.

Ya ce kungiyar ta yi barazanar sake tsunduma yajin aikin ne saboda shi ne matakin karshe da za ta iya dauka kuma shi ne kadai yaren da gwamnatin take fahimta.

Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya ce kungiyar za ta bi dukkan matakan da suke cikin doka wajen ganin ta kai ga gaci, ciki har da tattaunawa da jama’a da kuma gwamnati.