Home Labaru Zuba Jari: Shirin Gudanar Da Taro A Jihar Kaduna Ya Kammala

Zuba Jari: Shirin Gudanar Da Taro A Jihar Kaduna Ya Kammala

9
0
KADInvest

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce duk da ƙalubalen tsaro da take fama da ita a jihar, kawo yanzu ta samu sama dala biliyan biyu da masu zuba jari suka kawo jihar daga wasu kasasashe.

Shugabar hukumar bunkasa zuba hannayen jari ta jihar Kaduna wato KADIPA, Umma Yusuf Aboki, ta ce yanzu haka an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da wani babban taro na masu zuba jari wato KADInvest a jihar ta Kaduna.

Umma Yusuf tace taron wanda shi ne karo na shida ana sa ran mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne  zai jagoranta.