Home Labaru Mataimakin Shugaban Kasa Ya Bukaci Matasa Su Shiga Siyasa

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Bukaci Matasa Su Shiga Siyasa

101
0

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shawarci matasan kasar nan su shiga siyasa domin samun dammar kawo sauyin da suke fatan gani.


Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wurin wani
taro da ya gudana ta yanar gizo inda ya zanta da wasu ‘yan
najeriya da ke cikin shirin Mandela Washington na matasan
shugabannin Afrika.


Osinbajo, ya bada misali da lokacin da yake gwagwarmayar
kungiyoyin fararen hula kafin daga baya ya tsunduma cikin
siyasa inda ya zama kwamishinan shari’a a jihar Legas.


Yace da bai shiga gwamnati ba da har yanzu yana aiki da
kungiyoyin fararen hula, kuma da ya yi wani abu mai kyau,
amma ba zai iya kawo sauyin da kasar nan ke bukata ba.