Home Labaru Uwargidan Erdoğan Ta Bude Cibiyar Musayar Al’adun Turkiyya A Abuja

Uwargidan Erdoğan Ta Bude Cibiyar Musayar Al’adun Turkiyya A Abuja

15
0

Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdoğan, ta kaddamar da wata cibiyar koyar da al’adun Trukiyya a nan babban birnin tarayya Abuja.


A yayin bude cibiyar mai suna Yunus Emre dake yankin
Maitama, Mai dakin shugaban ta samu Rakiyar matar
mataimakin shugaban Kasa Dolapo Osinbajo, da kuma ministar
ba da agaji ta Najeriya Sadiya Umar Farouq.


Emine ta ce gina wannan cibiya wani yunkuri ne na kara kulla
alaka ta fuskar al’adu tsakanin Turkiyya da Najeriya.


Cibiyar da aka sanyawa sunan tsohon mai kasidar nan na karni
na 13 Yunus Emre, za ta rika wayar da kan ‘yan Najeriya ne
game da al’adun Turkiyya.


Har ila yau cibiyar zata kuma taimaka wajen koyon yaren
Turkiyya da sauyin hikimomi da al’adu da kimiyya da ilimi
tsakanin kasashen biyu.


Da take jawabi a wurin bude cibiyar Emine Erdoğan ta ce
mutanen kasarta na yi wa Afrika kallon wata tauraruwa da ke
tashe a karni na 21, inda tace akwai dalibai kimanin 14,000 da
ke samun tallafin Turkiyya.