Home Labaru Matsalar Tsaro: An Dakatar Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Daga Kaduna Zuwa Abuja

Matsalar Tsaro: An Dakatar Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Daga Kaduna Zuwa Abuja

190
0

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa saboda matsalar tsaro.


Hukumar ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet a ranar
Alhamis din nan.


Hakan na zuwa ne bayan da aka kai wa wasu jiragen ƙasa dake
jigilar Fasinja daga Abuja zuwa Kaduna hari har sau biyu a jere.


Harin farko ya faru ne a ranar Laraba yayinda aka kai hari na
biyu da safiyar ranar Alhamis din nan.


Wasu da lamarin ya rutsa da su sun ce harin ya jawo lalacewar
layin dogon da jirgin ke bi.


Tsohon Dan majalisar Dattijjai daga Jihar Kaduna Ya tabbatar
da kai hari kan jirgin a ranar Laraba inda yace jirgin ya taka
nakiya ne, sannan aka buɗe masa wuta.

Hukumomin sun ce lamarin ya faru ne tsakanin Rijana da Dutse,
inda harin ya lalata hanyar da jirgin ke bi.


Anata bangaren Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da tabbaci cewa
’yan ta’adda ne suka kaiwa Jirgin dake kan hanyarsa ta zuwa
Kaduna daga Abuja.

Babban jami’in hukumar Fidet Okhiria yace hukumar na
gudanar da bincike a kan lamarin. Inda ya yi watsi da rahotannin
da ke cewa ’yan ta’adda ne suka kai harin.

Leave a Reply